Ɗan wasan Paris Saint-Germain Lionel Messi, na tunanin komawa Al Nassr, ta Saudi Pro League, SPL.
Wannan shi ne kulob din da ke biyan fitaccen dan wasan gaba Cristiano Ronaldo.
Rahoton na La Gazzetta Sport ya ce dan wasan mai shekaru 35 yana son kulla kyakkyawar alaka da Ronaldo a Saudiyya.
Karanta Wannan: A shirye mu ke mu tunkari abokan hamayyar mu – Super Falcons
Messi ya yi la’akari sosai da daukar matakin yayin da yake shirin tafiya na gaba da kwantiraginsa a PSG zai kare a bazara.
A halin yanzu dai Messi bai ji dadin zama a PSG ba saboda halin da magoya bayan kungiyar suka yi a wasannin baya bayan nan da suka yi na ficewa daga gasar zakarun Turai.
Rahotanni sun bayyana cewa wata kungiyar SPL ta Al-Hilal tana sha’awar siyan Messi kuma tana iya shiga takarar neman dan wasan na Argentina.