Hukumomi a Ukraine sun bayyana cewa akwai rahotannin da ke cewa an sake kai wasu hare-hare a wuraren da ke makwaftaka da tashar nukilitya ta Zaporizhzhia.
Babu tabbaci kan adadin waɗanda suka jikkata ko kuma girman ɓarnar da aka yi.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya ƙara jaddada cewa tashar nukiliyar wadda Rasha ta mamaye na cikin hatsari.
Mista Zelensky dai ya gode wa ma’aikatan makamashi da ke aiki a tashar kan ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata duk da halin da suke ciki.


