Akwai yiwuwar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta cire sunan dan takarar gwamnan APC na jihar Bauchi, Abubakar Sadique Baba, idan har ta amince da bukatar da aka gabatar mata game da hakan.
Abubakar Sadique Baba ya riƙe muƙamin babban hafsan sojan sama kafin ritayarsa da kuma shiga siyasa.
Ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a Bauchi ne, bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani wanda aka gabatar a cikin watan Mayu.
Bukatar neman cire sunan Abubakar Sadique a matsayin ɗan takara na cikin wata takarda da wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubutawa shugaban hukumar INEC.
Kungiyar ta yi koken cewa, dan takarar bai gabatar da cikakkun takardunsa ba ga hukumar zaben, kamar yadda doka ta tanada.
A cewar kungiyar, Air Marshall Abubakar bai sanya wasu muhimman takardunsa waɗanda za su tabbatar da bayanan da ya cike a form din INEC mai suna EC 9 ba.