Shugaban yankin Zaporizhzhia na Ukraine ya sanya hannu a kan wata manufa da za ta bari a gudanar da zaben raba gardama a yankin domin shiga kasar Rasha, kafar yaɗa labaran RIA Novosti ta rawaito.
Kudancin Zaporizhzhia na karkashin ikon Rasha, kuma shi ne yanki na gaba da hankali ya koma kai a yaƙin yayin da kamfanin sarrafa makamashin nukiliyar Ukraine na Zaporizhzhia yake shan luguden wuta.
Rasha da Ukraine duka sun zargi juna akan kaiwa kamfanin nukiliyar hari, lamarin da ya jawo gargadin “babban bala’in nukiliya” daga hukumar nukiliyar kasa da kasa. In just BBC.