Mahukunta a Najeriya sun ce babu tsammanin gano ko da mutum guda da rai cikin masu hakar ma’adanan da kasa ta ruftawa a jihar Neja.
Wannan lamari ya faru ne a yankin Galkogo na jihar sama da sati uku ke nan da suka gabata
Honorable Yussif Shu’aibu Mani Sule Jaa, shugaban kungiyar ma’aikatan hakar ma’adanai ta kasa a Najeriya reshen jihar Naija ya ce zai yi wuya a iya tantance adadin mutanen da kasa ta danne a ibtila’in kasancewar mutumin da ake tunanin yana da bayanai game da ma’aikatan da ake aiki a wurin shi ma yana cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Sai dai a cewarsa, bayanai sun nuna mutanen da lamarin ya rutsa da su sun zarce 30.
Jami’in ya kara da cewa shawarar da suka bayar duba da cewa lokaci na kurewa shi ne a yi kokarin zakulo gawarwakin daga karkashin kasa don yan uwansu su iya shaida su, “wadanda za a iya masu sallah, a yi masu.” in ji shi.
A iya saninsa a cewarsa, ba ya tsammanin an yi wani abu don fitar da mutanen daga inda suke ba.
Ya bayyana cewa “dutse ne ya rushe da su a cikin kogon da suke ciki, ka san aikin ma’adinai, rami aka yi a cikin dutsen, sannan saman an barshi, kasan kuma an riga an bude, da ya tashi rushewa, sai ya rushe daga sama ya rufe da su ciki.
Ya kara da cewa “kusan kwana ashirin da wani abu a ce mutum na kunshe a rami – ba abinci ba ruwa ba iska, tana iya daurowa a bude a samu wasu da rai, kasan Allah Sarkin iko.” kamar yadda ya ce.