Kakakin rundunar sojin Isra’ila (IDF) Daniel hagari ya ce ƙasarsa da ƙungiyar take yaƙi ba da al’ummar Lebanon ba.
Yayin da yake jawabi ta gidan talbijin na ƙasar, jim kaɗan bayan da ƙungiyar Hezbolla ta tabbatar da mutuwar jagoranta Hassan Nasarallah.
Ga wasu daga cikin batutuwan da ya taɓo a lokacin jawabin nasa.
- Hagari ya bayyana Nasrallah da cewa “yana cikin manyan maƙiyan Isra’ila”
- Ya ce an kashe Nasrallah a wani “shiryayyen” hari da sojojin saman Isra’ila suka ƙaddamar a birnin Beirut ranar Juma’a.
- Yanzu haka sojojin Isra’ila na kai hare-hare kan gine-ginen Hezbollah a Lebanon, in ji Hagari
- Ya ƙara da cewa sojojin ƙasarsa na cikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci.
- Mun kuma haramta taruwar jama’a da ya wuce mutum 1,000 a tsakiyar Isra’ila.


