Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin sabon Alkalin Alkalan na kasa (CJN).
Wannan ci gaban dai ya biyo bayan tantance sa ne da kwamitin koli ya yi a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba.
A yayin tantancewar, Mai shari’a Ariwoola ya amsa tambayoyin da Sanatoci suka yi masa.