Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta fitar da sanarwar yajin aikin a fadin kasa, domin neman sauya farashin famfon man fetur da sauran manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun kungiyar ta NLC, Mista Ben Upah ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Laraba.
A cewarsa, yajin aikin na kasa baki daya zai fara ne daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023.
“Eh, za a fara yajin aikin a fadin kasar a ranar 2 ga watan Agusta 2023. Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sanarwar hakan”, in ji shi.