A yau Alhamis ne jigilar mahajjatan Najeriya kashin farko na maniyyata aikin hajjin shekarar 2022 zuwa kasar Saudiyya zai tashi daga filin jirgin saman Maiduguri.
Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, ta amince da wasu kamfanonin jiragen sama guda uku da suka hada da Max Air, Azman Air, da Flynas don kai maniyyata 43,008 da aka ware wa kasar zuwa kasa mai tsarki.
Daya daga cikin kamfanonin jiragen sama na kasar, Max air, da ya shirya jigilar maniyyata zuwa jirgin farko, ya shirya tura jiragen Boeing 747-400 guda biyu domin gudanar da aikin.
Babban kamfanin jirgin na cikin gida zai kai maniyyata 16,000 daga jihohi 13 na tarayya da suka hada da Taraba, Kogi, Niger, Kwara, Jigawa, Katsina, Benue, Plateau, Borno, da Nassarawa. In ji Guardian.