fidelitybank

Da Dumi-Dumi: ‘Yan tadda sun kashe mutane biyar a hanyar Birnin Gwari

Date:

Akalla mutane biyar ne ‘yan ta’adda suka kashe a kauyen Manini da ke kusa da Kuriga, a kan hanyar Brinin Gwari zuwa Kaduna.

Kuriga dai ya na karamar hukumar Birnin Gwari ne a jihar Kaduna, wanda ya yi kaurin suna wajen ‘yan fashi.

Shugaban kungiyar Brinin-Gwari Vanguards for Security and Good Governance, Alhaji Ibrahim Abubakar Nagwari, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, daga cikin wadanda suka mutu akwai Saifudeen Lawal Isa, wani namijin Brinin-Gwari, mutum daya dan Kuriga da kuma wasu biyu daga Udawa.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma, inda ‘yan ta’addan suka bude wuta kan masu ababen hawa a kan babbar hanyar har sau uku, inda ya ce, wasu mata biyu da wasu biyar sun samu raunuka da harsashi.

Ya kara da cewa, “yan ta’addan sun kone kurmus da wata tanka da ke jigilar man fetur zuwa BrininGwari a daidai wurin da ake kashe mutane a Manini.”

A cewarsa, “harin da kashe-kashen da ake yi a yankin na kullum ne”, yana mai jaddada cewa, ya kara dagula zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar Brinin zuwa Gwari zuwa Kaduna.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp