Rahotanni na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun tare motar jihar Katsina ta KTSTA, sun kashe direban, sun tafi da fasinjoji.
Labarin da muke samu yana nuni ne da cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare motar hukumar sufuri ta jihar Katsina, KTSTA a kan hanyar ta na zuwa Jibia da rana a ranar Lahadi.
Kamar yadda Katsina Post ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun kashe direban motar, sannan kuma sun kwashe fasinjojin cikin motar da ba’a san yawan su ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.