Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wata mata ‘yar shekara 29 mai suna, Miss Chinwendu Umegbaka, bisa zargin sace yaron makwabcinta a Nwawulu Sreet, Okpoko, Onitsha.
An kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar da karfe 4:30 na yamma a Okpoko.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu ya ce, “’Yan sanda sun kama wata Miss Chinwendu Umegbaka ‘yar shekara 29, ‘yar asalin Isinkwo Abaomege a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi kan zargin satar yara a Okpoko, Onitsha. , Jihar Anambra.”
A cewarsa, binciken farko na ‘yan sanda ya nuna cewa, wanda ake zargin makwabci ne ga iyayen yaron.
Ya ce, lokacin da aka kama wadda ake zargin, da farko ta musanta cewa, ta san inda yarinyar mai shekaru 3 take.
Kakakin ‘yan sandan ya kuma kara da cewa, da aka ci gaba da yi mata tambayoyi ta amsa laifin satar yaron da nufin sayar da ita.
Sai dai ya bayyana cew,a an dawo da yaron kuma an mika shi ga iyayen sa.