Wasu ‘yan Najeriya sun samu damar tsallakawa zuwa kasar Poland mai maƙotaka da kasar Ukraine.
Wani da ake zaton jami’in jakadancin Najeriya ne a Poland ya wallafa wani bidiyo a shafin Twitter yana mai cewa aƙalla ‘yan Najeriya bakwai ne suka isa sansani ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin Poland ta ware.
“Na samu damar ganin ‘yan Najeriya bakwai a nan, yanzu haka suna cin abinci. Idan sun gama za mu ɗebe su zuwa wani wurin daban,” a cewar wanda ya ɗauki bidiyon da hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta wallafa.
Hukumomi a Najeriya na shawartar ‘yan ƙasar su tsallaka ƙasashen Poland da Hungary masu maƙotaka da Ukraine tun bayan Rasha ta fara kai hare-hare a ranar Alhamis.