fidelitybank

Da Dumi-Dumi: ‘Yan majalisar dokoki Kano 9 sun koma jam’iyyar NNPP

Date:

Mambobin jam’iyyar PDP tara a majalisar dokokin jihar Kano, sun fice daga jam’iyyarsu zuwa New Nigeria People Party (NNPP).

Sakataren yada labaran Majalisar, Uba Abdullahi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce ‘yan majalisar da abin ya shafa sun aike da wasika ga shugaban majalisar, inda suka sanar da majalisar cewa sun sauya sheka.

A cewarsa, wasu daga cikin dalilan da ‘yan kungiyar suka bayar na da alaka da rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP a matakin jiha da kasa baki daya.

Mambobin da abin ya shafa sun hada da; Isyaku Ali Danja (Mazabar Gezawa), Umar Musa Gama (Mazabar Nassarawa), Aminu Sa’adu Ungogo (Mazabar Ungogo), Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa (Mazabar Dala) da Tukur Muhammad (Mazabar Fagge).

Sauran su ne; Mu’azzam El-Yakub (Mazabar Dawakin Kudu), Garba Shehu Fammar (Mazabar Kibiya), Abubakar Uba Galadima (Mazabar Bebeji) da Mudassir Ibrahim Zawaciki (Mazabar Kumbotso).

A ranar 29 ga watan Afrilu ne majalisar ta sanar da sauya sheka dan majalisar wakilai Salisu Maje Ahmed Gwangwazo daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC sakamakon rikicin cikin gida na jam’iyyar.

PlatinumPost ta rawaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar PDP a jihar kwanan nan ya koma jam’iyyar NNPP, inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp