Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida mai suna Mista Chuks Onuha a gidansa da ke Umuhu, Ohuhu a karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia.
Rahotanni sun nuna cewa, Onuha tsohon wakilin jaridar Sun ne a jihar Abia.
Onuha dai yana cin abinci ne tare da iyalansa a daren ranar Talata inda ‘yan bindigar suka kutsa cikin gidansu tare da dauke shi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba, inji rahoton Daily Sun.
An kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansa inda suka bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 10 a safiyar ranar Laraba.
Matarsa kuma ta tabbatar da faruwar lamarin lokacin da aka tuntube ta a waya. Don haka ta yi kira ga wadanda suka yi garkuwa da su da su saki mijinta ba tare da wani sharadi ba domin kare ‘ya’yansu.
A ranar Talata, SaharaReporters ta kuma ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sanye da kakin ‘yan sanda sun kai hari a babban birnin tarayya Abuja, sun yi garkuwa da mata masu juna biyu uku, yara biyu da wasu 12 a Abuja.