Wasu ‘yan bindiga sun kutsa gidan shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN, ta Jihar Edo, Abdullahi Baba-Saliu, inda su ka saceĀ shi da karfi da yaji, sannan suka bindige daya daga cikin direbobinsa har lahira tare da jikkata masu tsaronsa da dayan direbansa.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta bakin mai magana da yawun ta, Bello Kotongs ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta kuma ce, suna kokarin ceto wanda aka sace din.
The Punch ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, kamar yadda rahotanni suka nuna.