Wasu ‘yan bindiga sun sace Bishop na darikar Anglican, Rabarand Oluwaseun Aderogba da ke Jebba a Jihar Kwara ta Tsakiyar Najeriya tare da matarsa da dirabansa.
Gidan talbijin na Channels TV ya rawaito cewa an sace mutanen ne ranar Lahadi da maraice a kan hanyar Oyo/Ogbomoso da ke Jihar Oyo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da sace mutanen a wata sanarwa da ya fitar.
Ya kara da cewa wani mutum mai suna Rabarand Adekunle Adeluwa ne ya kai wa ‘yan sanda labarin sace takwaransa.
A cewar Osifeso, binciken farko ya nuna cewa motar limamin cocin ce ta samu matsala a yayin da suke tafiya daga Yewa da ke Jihar Ogun zuwa Jebba a Jihar Kwara.
Ya kara da cewa an bai wa mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan yankin umarnin gano da kuma ceto mutanen.