An tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu biyu ke kwance a asibiti, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Garin Gabas da ke karamar hukumar Malam Madori a jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawal Shiisu, wanda ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Asabar, ya ce, ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutum guda.
A cewarsa, “Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 2:30 inda ‘yan bindiga suka kai hari Garin Gabas a garin Malam Madori inda suka harbe mutum hudu kafin su tafi da wani Musa Malili dan shekara ashirin da biyu.
“Biyu daga cikin hudun da aka harba sun mutu a asibiti yayin da sauran biyun ke karbar magani a asibiti,” ASP Shiisu ya bayyana.
Ya kara da cewa, ‘yan sanda suna yin duk mai yiwuwa don ganin sun kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi, ya kuma bukaci ‘yan kasar da su kai rahoton duk wani motsin jama’a da ke damun al’ummarsu.