Rahotanni daga jihar Katsina, sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani ayarin motocin ‘yan kasuwa da na sojojin da ke musu rakiya.
Wani rahoton na cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a san inda wasu sojojin suka shiga ba. In ji BBC.
Harin ya auku ne tsakanin kauyen Shimfida da garin Jibia, wurin da ke fuskantar karuwar hare-hare daga barayin daji a ‘yan makonnin da suka gabata.