A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna (KDSG), ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan masu ibada, inda suka kashe mutane uku tare da raunata wasu biyu a karamar hukumar Kajuru da ke jihar.
Ya bayyana cewa, a kauyen Rubu, ‘yan bindigar sun kai hari a cocin Maranatha Baptist da Cocin St. Moses Catholic Church.
“An tabbatar da mutuwar mutanen yankin uku a hare-haren, kuma mutane biyu sun ji rauni – daya daga cikinsu mace ce da mace daya da ba a tantance ba.
“An kuma yi garkuwa da wasu mutanen yankin da ba a tantance adadinsu ba,” a cewar rahotanni.
“‘Yan fashin sun yi awon gaba da shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja daga kauyukan,” in ji shi.