fidelitybank

Da Dumi-Dumi: ‘yan bindiga sun kai farmaki wurin da ake zaben fidda gwani

Date:

Wasu ‘yan bindiga sama da 10 da ba a san ko su waye ba, sun kai farmaki makarantar ‘yan mata ta Anglican Grammar School, Ozoro, hedkwatar karamar hukumar Isoko ta Arewa a jihar Delta, wurin da ake ci gaba da gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP na mazabar Isoko ta Arewa.

A cewar SaharaReporters, ‘yan bindigar sun taru ne a wurin da kananan motoci kirar Toyota Sienna guda uku, jim kadan bayan an bayyana sakamakon zaben fidda gwani da wakilai da ‘yan takara suka bar wurin. Daga nan ne suka fara harbin iska ba kakkautawa yayin da ‘yan jam’iyyar da magoya bayansu da jami’an tsaro suka yi ta tururuwa zuwa wurin tsira.

An kammala zaben lami lafiya inda mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Bernard Odion ya lashe zaben da kuri’u 23 inda ya doke dan takara Jude Ogbimi wanda ya samu kuri’a daya. Shugaban karamar hukumar, Emmanuel Egbabor, wanda ya samu kuri’u 8 ne ya zo na biyu.

SaharaReporters ta tattaro cewa, gabanin zaben shugaban karamar hukumar Isoko ta Arewa, Christian Iteire a ranar Juma’a ya yi zargin cewa, ya yi awon gaba da wakilan wucin-gadi tare da yi musu sansani a wani otal domin hana sauran masu son samun damar ganawa da wakilan kafin zaben.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp