fidelitybank

Da Dumi-Dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki kan jami’an JAMB

Date:

Wasu gungun ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba a ranar Larabar, sun kai farmaki kan jami’an hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB a jihar Legas.

Rahotannin da ke isowa Naija News a wancan lokacin, sun tabbatar da cewa maharan da tsakar daren ranar Talata, sun kai hari a otal din Mabila da ke Ikorodu a jihar Legas, inda suka far wa jami’an hukumar jarabawar da fashi da makami.

An ce sun kashe mai gadin otal din ne kafin su kai samame dakunan da ke cikin otal din.

Da yake tabbatar da faruwar harin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya shaidawa manema labarai cewa, nan take aka mayar da jami’an hukumar ta JAMB zuwa wani wuri mai tsaro biyo bayan faruwar lamarin.

“Wani Farfesa Odunsi, jami’in hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ya sauka a otal din an yi masa fashin wayoyinsa guda biyu, HP Laptop daya da kudi N20,000.

“Hakazalika, wasu mata biyu jami’an JAMB da suka sauka a otal din, an yi musu fashin wayoyin hannu da kayan kwalliya,” inji shi.

Ma’aikacin kofar otal din a cewar jami’an tsaro ya yi kokarin takaita ‘yan bindigar amma an harbe su a cikin lamarin.

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp