Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su wanene ba, sun kashe wasu mutane biyu da ake kyautata zaton mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Ebonyi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Mkpuma Akataka da ke karamar hukumar Izzi a jihar.
Jaridar DAILY POST ta samu labarin cewa taron jam’iyyar APC na gudana ne da yammacin ranar Juma’a a cikin al’umma inda ‘yan bindigar suka far wa wurin inda suka bude wuta.
‘Yan ta’addan wadanda aka ce adadin su biyu ne, sun zo ne a kan babur, inda suka yi sauri su ka tashi, bayan sun kammala aikinsu.
An tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu biyu ke karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme da ke Abakaliki.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Chris Anyanwu ya zuwa yanzu bai bayar da amsa ba.


