Akalla jami’ai hudu ne aka harbe a wani hari da aka kai ofishin ‘yan sandan Atani da ke karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra.
Rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da sanyin safiyar Laraba.
A cewar wata majiya daga Atani, maharan sun isa yankin ne da misalin karfe 1:30 na safiyar Laraba.
Majiyar ta ce, ‘yan sanda hudu da suka hada da mace daya sun rasa rayukansu a harin.
An dai sha kai hare-hare a ofisoshin ‘yan sanda da wasu cibiyoyin gwamnati a Anambra tun bayan da Farfesa Chukwuma Soludo ya hau kujerar gwamna makonni uku da suka gabata.
Soludo ya ci gaba da ba da tabbacin cewa, wadanda ke da alhakin kai hare-haren za a hukunta su ba.
Da yake tabbatar da harin na baya-bayan nan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce, “‘yan ta’addan sun zo ne da misalin karfe 1:00 na safe, kuma ba mu yi sa’a ba, ‘yan sanda hudu ne suka mutu”.
Ya ce, kwamishinan ‘yan sandan, CP Echeng Echeng, da jin labarin harin, nan take ya tara jami’an rundunar daga sassa daban-daban zuwa yankin.