Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun yi wa wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda kwanton bauna a karamar hukumar Oyigbo ta jihar Ribas.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe dan sandan, wanda ba a iya tantance sunansa ba, yayin da yake dawowa daga aiki a ranar Laraba.
An ce wanda aka kashe din ya rasu ne a wani asibiti da ba a bayyana ba inda aka garzaya da shi domin duba lafiyarsa.
Jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sanda, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da kisan.
Iringe-Koko ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Friday Eboka, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.