An kashe wani Sufeton ‘yan sanda mai suna, Temenu Boluwaji, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Okuta Elerinla da ke Akure, babban birnin jihar Ondo.
An kai harin ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, SP Fumilayo Odunlami, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce, ‘yan sandan da ke bakin aiki sun yi artabu da maharan, inda suka hana su shiga ofishin.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Oyeyemi Oyediran, ya umarci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta dauki nauyin lamarin tare da tabbatar da kama wadanda suka aikata laifin.