Wasu yan bindiga sun kashe mutane sama da shida a yankin Karal Sunkuma Kona, wani bangare na yankin tare da tarwasta al’umma mazauna yankin na Kararr dake karamanr hukumar Gasol a jihar Taraba.
Wani dan yankin da abin ya faru ya shaidawa muryar Amurka tare da alkawarin cewa, da misalin karfe 12 da rabi ne ‘yan bindiga suka kawo musu harin da ya yi sanadiyar mutuwan mutane sama da shida a yankin nasu.
A nasu bangaren jami’an ‘yan sanda na jihar Taraba tabakin kakakin rundunar, DSP Usman Abdullah, ya ce sun hada rundunar su ta hadin gwiwa, domin ganin an kawo karshen ‘Yan bindigar a jihar Taraba gabaki daya.