Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan sanda da ba a tantance ba a Ogidi, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
The Nation ta rawaito cewa, ‘yan bindigar a wani shingen bincike na ‘yan sanda da ke cikin harabar gidan al’ummar yankin, sun kuma kori mutane.
Wani mazaunin unguwar ya ce: “Sun dade suna jira har sai da suka ga daya daga cikin ‘yan sandan, wanda suka harbe shi, suka kwace masa bindigar AK 47, kafin daga bisani suka gudu.”