Rahotanni na nuni da cewa, wasu mutum biyu daga cikin tawagar mutane uku ta ‘yan ta’adda da sun gamu da ajalinsu a hannun mutanen gari.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, mutane sun yi ram da ‘yan ta’addar ne yayin da suka kai hari wani garejin gyaran mota dake kan babbar hanyar Badagry a jihar Legas, da misalin Æ™arfe 6:00 na safiyar nan.
Wani shaidan gani da ido ya ce, waÉ—an da ake zargin sun jima suna aikata ta’addanci a yankin Okoko, Igbolerin, Iyana da sauran wuraren dake kewaye.