An samu rudani jiya a jihar Imo, bayan da rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun kai harin bam a babbar kasuwar Izombe da ke karamar hukumar Oguta a jihar.
An yi zargin cewa ’yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne suka aiwatar da wannan danyen aikin da suka sanya dokar zama a gida a yankin.
Naija News ta rawaito cewa, a kalla motoci biyu ne ‘yan ta’addan suka kona sua. Lamarin da ya faru a cewar wani mazaunin garin da ya zanta da Daily Sun, ya sanya ‘yan kasuwa da kwastomomin da ke kasuwar suka rika tsira da rayukansu.
Majiyar ta shaida wa kafar yada labarai cewa, tun da farko ‘yan bindigar sun ziyarci kasuwar ne, domin gargadin ‘yan kasuwar kan illar fitowar su a ranar Litinin da ta gabata kan kasuwancinsu.
Bayan ‘yan mintuna kadan, an ce ‘yan bindigar sun sake tayar da zaune tsaye, inda suka kona motoci biyu da wuta a cikin kasuwar, lamarin da ya haifar da mummunar barna kafin a jefa bam a kasuwar.
Mutane da dama a cewar rahoton sun samu raunuka yayin da suke kokarin tserewa hatsarin.
“Sun zo ne suka jefa bam a cikin kasuwar, kowa ya fara gudu don tsira; sun zuba mai a kan motoci biyu kuma ko’ina ya tashi da wuta,” inji majiyar.