Rundunar sojin Ukraine a ranar Juma’a, ta ce, ta nutsar da wani jirgin ruwan Rasha a cikin tekun Black Sea.
An ce jirgin ruwan na kan hanyarsa ta mayar da sojojin da suka mamaye tsibirin Snake mai matukar muhimmanci.
Rundunar Sojan Ruwa ta Ukraine ta ce, “Tsarin jirgin ruwa na Bahar Black Sea”Vasiliy Bekh” an kai shi ne a cikin Tekun Bahar a yayin jigilar alburusai, makamai da ma’aikatan jirgin ruwan Black Sea zuwa Tsibirin Snake.” a cewar CNN.
Rundunar sojin ruwa ta yi ikirarin cewa, jirgin yakin na ruwa mai suna tug, yana da na’urar makami mai linzami na “TOR” a cikin jirgin.
A cewar shafin Marine Traffic, jirgin ruwan ya bar Sevastapol, a Crimea, a daren Talata.