fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Tsohon hadimin Ganduje ya fito takarar gwamnan Kano

Date:

Salihu Tanko-Yakasai, tsohon mai taimakawa gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano kan harkokin yada labarai, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zabe mai zuwa na 2023.

Tanko-Yakasai ya bayyana haka ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Talata.

Ya ce, sanarwar tasa a hukumance za ta gudana ne a ranar Juma’a, inda ya kara da cewa zai tsaya takara a jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP).

“Da sunan Allah na dogara ga Allah; babu karfi sai ga Allah. Yan uwa da abokan arziki da masoyana, wannan shine in sanar daku aniya ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kano karkashin babbar jam’iyyar mu ta PRP. Sanarwar ta a hukumance za ta faru a wannan Juma’a, ”ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hakan na zuwa ne makonni bayan da ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar APC.

A watan Fabrairun 2021, Ganduje ya kori Tanko-Yakasai saboda “ci gaba da maganganun da ba a kiyaye ba” da kuma sukar Shugaba Muhammadu Buhari.

Tanko-Yakasai, yayin da ya fice daga jam’iyyar APC a watan Maris, ya ce jam’iyyar ta kasa cika alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya a yakin neman zabe.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...

Ni da Wike tif da taya ne – Fubara

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce, babu...

Za a yi jana’izar Dantata a ranar Litinin

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid,...

Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam da tabbatar da dimokuraɗiyya...

Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan Dantata

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyarsa...
X whatsapp