A ranar Talata 17 ga watan Disamba, 2024 ne shugaban kasa Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar, inda ya bayyana cewa shugaban kasar ya aike da sako kan hakan.
“Shugaban kasa ya bayyana aniyar sa ga majalisar dokokin kasar na gabatar da kasafin kudin 2025m ga zaman hadin gwiwa na majalisar kasa a ranar 17 ga Disamba, 2024,” in ji shi.
Tun da farko Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya sanar da kasafin kudin wanda ya kai Naira tiriliyan 47.9.