Dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ya zama dan takara a jami’yyar, bayan ya samu kuri’u 1,271 mafi rinjaye a zaben.
Atiku Bagudu gwamnan Kebbi, shi ne wanda ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 1,271.
Tinubu ya kayar da Osinbanjo mataimakin shugaban kasa da Rotimi Amaechi da Ahmad Lawan da kuma Yahaya Bello.