Zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya, bayan hutun da ya yi a Turai.
Tinubu, wanda ya yi tattaki makonni biyu da suka wuce ya isa kasar ne a ranar Asabar.
Sanata Godswill Akpabio, Gwamna Abdullahi Ganduje da sauran ‘yan jam’iyyar APC ne suka tarbe shi.
Ya ce ya kai ziyarar aiki ne domin duba shirye-shiryen rantsar da shi, da ganawa da manyan masu saka hannun jari da kuma shirya kasar nan don gudanar da harkokin kasuwanci.
Sanarwar ta ce “A yayin ziyarar, zababben shugaban kasar zai yi hulda da masu zuba jari da sauran manyan abokan hulda da nufin tallata damar zuba jari a kasar da kuma shirye-shiryen gwamnatinsa don ba da damar yanayin kasuwanci mai kyau ta hanyar manufofi da ka’idoji,” in ji sanarwar.