Tawagar da Ecowas ta tura don sasanta rikicin siyasar Nijar ta isa Yamai, babban birnin ƙasar a yau Asabar.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.
Ana sa ran za su tattauna da jagoran mulkin sojan, Janar Abdourahmane Tchiani, game da yadda za a mayar da mulki ga farar hula.
Ecowas na son sojojin su mayar da Mohamed Bazoum kan mulki, wanda suke tsare da shi tun 25 ga watan Yuli. A cewar BBC.