Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima.
Tawagar ‘yan majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakain majalisar Jibril Isma’il Falgore ne suka gabatar wa gwamnan sabuwar dokar a gidan gwamnatin jihar.
Da safiyar yau Alhamis ne dai majalisar ta yi wa dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 kwaskwarima, inda ta soke duka masarautun jihar biyar.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Gwamna ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa dokar masarautun Kano ta 2019.