Kungiyar Southampton, a ranar Lahadi, ta kori kocinsu, Nathan Jones.
Southampton ta kuma kori Kociyan Kungiyar ta Farko, Chris Cohen da Alan Sheeha.
Kulob din na Ingila, ya sanar da cewa Kociyan Kungiyar na Farko Rubén Selles ne zai jagoranci Southampton a wasansu na gaba da Chelsea a gasar Premier.
Southampton ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta gidan yanar gizon ta.
Korar Jones ta zo kasa da sa’o’i 24 bayan sun sha kashi a hannun Wolves da ci 2-1 ranar Asabar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar Kwallon Kafa ta Southhampton na iya tabbatar da cewa ta rabu da Manajan Tawagar maza na farko Nathan Jones.
“Kociyan kungiyar farko Chris Cohen da Alan Sheehan suma sun bar kungiyar.
“Kociyan kungiyar na farko Rubén Selles zai dauki nauyin atisaye tare da shirya kungiyar gabanin wasan da za su kara da Chelsea a karshen mako mai zuwa.”