Aƙalla mutum bakwai aka sanar da mutuwarsu a wani harin bam da dakarun Rasha suka kai a Ukraine, kamar yadda ƴan sanda a Ukraine ɗin suka sanar.
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa, wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke a Podilsk a wajen Odessa ya yi sanadin mutuwar mutum shida da kuma raunata mutum bakwai.
Haka kuma akwai mutum 19 da ba a san inda suke ba. Haka kuma an tabbatar da cewa mutum guda ya rasu a birnin Mariupol. In ji BBC.