fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Shugaban kasar Sri Lanka ya yi murabus bayan matsin lamba

Date:

Kakakin majalisar dokokin Sri Lanka, Yapa Abeywardena, ya ce, shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa, ya yi murabus daga mukaminsa a cikin tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Murabus din Mista Rajapaksa zai fara aiki ne daga ranar Laraba mai zuwa, don ba da damar samun sauyi cikin sauki.

“Ya bukace ni da in sanar da kasar cewa, zai yi murabus a ranar Laraba 13 ga wata, saboda akwai bukatar mika mulki cikin lumana.

“Saboda haka babu bukatar sake tayar da hankali a kasar, kuma ina kira ga kowa da kowa saboda kasar da ya wanzar da zaman lafiya, domin samun damar mika mulki cikin kwanciyar hankali,” in ji kakakin a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin.

Mista Abeywardena ya bayyana hakan ne bayan da wasu fusatattun masu zanga-zangar suka kai wa gidan Mista Rajapaksa da na dan uwansa tsohon firaminista Mahinda Rajapaksa hari.

Murabus din shugaban ya fi kawo karshen daular Rajapaksa, wacce ta mulki kasar sama da shekaru goma, fiye da kawo karshen matsalar jin kai da kasar ke fuskanta.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...
X whatsapp