Sarauniyar Denmark Margrethe II, ta sanar da yin murabus a jawabinta na sabuwar shekara da aka yaɗa kai-tsaye ta talabijin.
Za ta sauka daga muƙamin a ranar 14 ga watan Janairu, wanda zai zama shekara 52 daidai da zamanta sarauniya.
Babban ɗanta Yarima Frederik ne zai karɓi mulkin bayan saukarta.
Matar mai shekara 83, ita ce basarakiya mafi daɗewa a kan karaga a tarihin ƙasar da ke Turai, wadda ta hau mulki bayan mutuwar mahaifinta Sarki Frederik IX a 1952.