Sanatocin uku da aka zaba a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sun fice daga jam’iyya mai mulki.
‘Yan majalisar sun hada da Sanata: Ahmad Babba Kaita (Katsina ta Arewa), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi ta Kudu), da Francis Alimikhena (Edo ta Arewa).
Yayin da Babba Kaita da Alimikhena suka koma jam’iyyar adawa ta PDP, Gumau, a daya bangaren, sun koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Sanarwar murabus din nasu da sauya shekar nasu na kunshe ne a cikin wasiku daban-daban guda uku da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata.
Sauya shekar da ‘yan majalisar uku suka yi ya rage yawan Sanatocin APC daga 70 zuwa 67 a zauren majalisar.