Sanatocin jam’iyyun adawa sun fice daga zauren majalisar dattawan a fusace, bayan da aka yi watsi da kudurin da suka gabatar na tsige Shugaba Buhari.
Gidan Talbijin na Channels TV na ƙasar ya ruwaito cewa ‘yan majalisar na jam’iyyun adawa sun bai wa shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida da ya kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.
Sun kuma yi barazanar fara batun tsige shugaban matukar ya kasa magance matsalar cikin wa’adin da suka ba shi.
Shugaban marasa rinjaye na majalaisar, Sanata Phillip Aduda ne ya gabatar da kududrin a gaban zauren majalisar, inda ya roki shugaban majalisar Ahmed Lawan da ya amince majalisar ta tattauna batun tsaro, da kuma na tsige shugaban kasar.
To amma shugaban majalisar dattawan ya ƙi amincewa da bukatar dan majalisar yana mai cewa sam-sam ƙudirin bai dace ba.