Dr Mohammed Barkindo, babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC), ya rasu.
A ranar Talatar da ta gabata ne ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa, inda shugaban ya karbe shi da cewa, ya zama jakadan da ya cancanta a Najeriya.
Mista Mele Kyari, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.
“Mun yi rashin mai girma Dakta Mohammed S Barkindo. Ya rasu da misalin karfe 11:00 na dare. ranar Talata.
“Tabbas babban rashi ne ga danginsa, NNPC, kasarmu Najeriya, kungiyar OPEC da kuma kungiyar makamashi ta duniya.
“Za a sanar da shirye-shiryen jana’izar nan ba da jimawa ba,” in ji Kyari.
Barkindo wanda shine sakatare janar na kungiyar OPEC mai barin gado yana Najeriya inda ya gabatar da jawabin shugaban a taron mai da iskar gas na Najeriya (NOG) da ke gudana a Abuja ranar Talata.
An haife shi a ranar 20 ga Afrilu, 1959 a Yola, Adamawa, Barkindo ya rike mukamin Sakatare Janar na OPEC tun ranar 1 ga Agusta, 2016 kuma zai yi rantsuwa a ranar 31 ga Yuli, 2022 bayan kammala wa’adinsa.
Ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a shekarar 1981, sannan ya yi digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci a Jami’ar Washington a 1991.