fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Romania ta baiwa daliban Najeriya damar karasa karatun su

Date:

Gwamnatin Romania ta yi tayin bai wa ɗaliban Najeriya damar ci gaba da karatu a jami’o’in ƙasar ta, bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake tafkawa a ƙasar, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Najeriya.

Babban sakatare a ma’aikatar, Gabriel Aduda, ya ce, ministan ilimi na Romania wadda maƙociyar Ukraine ce, shi ne ya bayyana hakan.

Mista Aduda ya ƙara da cewa, yanzu haka suna tattaunawa da sauran maƙotan ƙasashe kamar Poland da Hungary da Girka, domin su bai wa ‘yan Najeriya irin wannan damar.

‘Yan Najeriya kusan 2,000 ne aka tabbatar sun tsallaka ƙasashe maƙotan Ukraine a yunƙurinsu na samun mafaka daga yaƙin da aka fara fafatawa ranar 24 ga watan Fabarairu.

Tuni aka kwaso ‘yan ƙasar kusan 1,000 amma har yanzu akwai ɗalibai a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnati domin su koma gida. In ji BBC.88486138

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

A dawo da tallafin aikin Hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijawa kan harkokin ƙasashen waje...

A na fargabar mutuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari

Kamfanin dillancin labaru na AP ya rawaito cewa, shugaban...

An kwashe wasu daga cikin Gawarwakin da Jirgi ya fada cikin gidaje a Indiya

Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya (FAIMA), ta ce an...

Tinubu ya mayar da martani kan mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mayar da martani game...

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...
X whatsapp