Kamfanin labarai na UNIAN na ba da rahoton cewa wani makamin roka da aka harba a birnin Kharkiv ya faɗa kan wani gini na ‘yan sanda.
Wani bidiyo da aka wallafa a dandalin Telegram na wani jami’in gwamnatin Ukraine ya nuna ginin na ci da wuta.
Anton Geraschenko, wanda mai bai wa ministan harkokin cikin gida shawara ne, ya ce wani gini mallakar Jami’ar Karazin shi ma ya kama da wuta sakamakon harin.