Rasha ta harba makamai masu linzami da dama a filin jirgin saman Lviv da ke Yammacin Ukraine.
Lviv dai na kusa da kan iyakar kasar Poland kuma yakasance wajen da daruruwan dubban ‘yan gudun hijra ke neman mafaka.
Magajin garin birnin ya ce makamai masu linzamin sun fada kan wata masana’antar da ke gyare gyaren jiragen sama.
Ya ce, harabar masana’antar duk ta lalace.Tuni muka yanke shawarar kwashe duk wasu muhimman abubuwa da ke wajen.
Mutum guda ne kawai ya ji rauni kuma ba bu wanda ya rasa ransa.
Wasu hotunna bidiyo sun nuna yadda fashewar hayakin ya turnuke.
Jami’ai sun ce, mutum guda ya samu rauni. Filin jirgin saman shi ne na biyu mafi girma a Ukraine.