Gwamnan lardin Lviv, Makysm Kozytskyi, ya yi ikirarin cewa Rasha ta harba makamai masu-linzami hudu a lardin.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce “bayanan farko” da suka samu ne suka tabbatar da hakan.
Ya bukaci mazauna lardin su “zauna a gidajenku”.
Wakilin BBC, Toby Luckhurst, ya ce sun ji karar manyan fashewa akalla biyar a yammacin Lviv, birnin da ke kan iyakar Ukraine da Poland.