A ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Anambra, Dokta Peter Obi ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party.
Obi ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa ne bayan da dan takarar shugaban kasa, Farfesa Pat Utomi ya janye masa.
An gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a garin Asaba na jihar Delta.
Joseph Faduri shi ma ya janye domin Obi ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Utomi ya ce Obi ya girme shi kuma yana da ikon aiwatar da canjin da ake bukata wanda kasar ke so.
Obi dai ya fice daga jam’iyyar PDP ne a makon jiya, sa’o’i 72 a zaben shugaban kasa na jam’iyyar.