Nwoba Chika Nwoba, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP a Jihar Ebonyi, a ranar Alhamis, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ne zai kasance abokin takarar Atiku Abubakar.
POLITICS NIGERIA ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne wani bangare na jam’iyyar Labour karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugabanta na kasa, Callistus Okafor, ya zabi Digar Ezenwafor a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake mayar da martani game da ci gaban, Nwoba ya ce “wani dabara ce ta bayar da dalilin da ya sa Obi ba zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour ba”.
“Tsohon Gwamna Peter Obi ne zai kasance abokin takarar Atiku Abubakar na PDP a zaben shugaban kasa na 2023,” Nwoba ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a Facebook.